A Bincike Karamar Hukumar Kano Municipal Inji Ibrahim Sanyi Sanyi

Ya dai kamata gwamnatin da zata karbi mulki hannun Gwamna Ganduje a 2019 da tai bincike akan yadda hukumar mulki ta KMC ta rabarda filayen Sani Abacha Stadium dake nan kan IBB Road. Wad’annan filayen dai an rabar dasune ga ‘yan majalisa, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa dss. Yanzu haka sai anyi namijin k’ok’ari kafin a zab’i stadium d’in domin buga wasannin kwallo na k’asa-da-k’asa sabili da irin wad’annan gine-ginen da suke gewaye da ita.

Bayan an gudanar da bincike, kamata yayi sabuwar gwamnati ta hukunta duk mai hannu a cikin wannan kama-karya sannan ta kwace filayen jama’a. Wannan shine adalci.

Irin wannan son zuciya ta hanyar fakewa da bunk’asa kasuwanci shi yasa duk kusan green areas da ake dasu a kwaryar Kano yanzu an mayar dasu shaguna, gidajen haya ko masallaci. Sannan kamar babu makarantu da ma’aikatun gwamnati akan titin Kasuwar Rimi zuwa Bakin Asibiti: duk shaguna na kama-wuri-zauna sun rufesu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: