An Kama Dagaci a Dawakin Tofa yana Sex da Matar Makwabcinsa

0
20

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani dagacin kauyen Dawakin Tofa ta Jahar Kano Sanusi Musa yana saduwa da matar makwabcinsa.

Majiyar  ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Dawakin Tofa, inda aka ce an kama wanda ake tuhuma rungume da matar wani.

Yayin da aka gurfanar da shi gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da mai shari’a Sheikh Atiku M. Bala yake alkalanci, wanda yanzu haka ya aika da Dagacin gidan yari har sai lokacin da aka kammala shari’ar da ake yi.

Mai gabatar da kara ya bayyanawa kotun cewa, jami’an Hisbah da ke aikin sintiri a Dawakin Tofa ne suka lura da wani abu na faruwa a cikin kangon wata rumfa, shigar su wajen ke da wuya sai suka tarar da wadanda ake zargin rungume da juna suna aikata fasikanci, aikin da yake laifi ne a dokar shari’ar Musulunci ta jihar da ta tanadi hukunci ga masu aikata fasikanci da karuwanci.

Dagacin kauyen Sunusi Musa ya amsa laifinsa, kuma ya roki kotu ta yi masa sassauci.

Alkalin kotun ya dage ranar cigaba da sauraron shari’ar zuwa mako na biyu na watan Maris mai zuwa.

Leave a Reply