Karyarka- Alqudus Bata Sayarwa Bacce- Palistinawa sun fadawa Trump

0
5

Shugaban kassar Amurika ya shiga rudani bayanda yan kassar palistinu suka ja daga sukayi watsi da wa’addin da Donald Trump ya bassu na sun janye karar da suka kai Yahudawa ko Amurika ta Janye taimakon kudin da takke bassu.

Yan Palistinun sun mayarwa da Trump martanin cewa birnin Alqudus bana na Sayarwa banne, kumma idan jayayyar da sukeyi akansa ne zai sa Amurika ta ja daga dasu, tau bisimillah.

Shugaban kassar na Amurika a watan da ya gabata ya sanya hannu a takarda da tacce Amurika ta yarda cewa Birnin Alqudus wadda Isrealla ta mamaye ta karfi da yaji a shekarar 1967 ya zama halataccen birnin na yahudawa ko ana so ko ba’a so. Tashar Aljazeera a rawaitowarta tacce Trump din yayi hakan ne da yarda wassu shugabanni na kasashen muslunci ciki harda mukaddashin Sarkin Saudiyya wanda a yunzu haka ya kulle yanuwan sa da yawa kuma ya kawo canje canje da ke sanya suadiyyar cikin rudani.

Tarayyar kungiyar kasahsen musulmai sunyi watsi da wannan wa’addin na Amurika inda sukayi allah wadai da yunkurin na Amurika. Kassar Malaysia ta sanya Dakarunta cikin shirin kota bacci inda shugaban dakarunta yacce a shirye takke takaiwa Musulman dakke cikin Alquds taimako idan dai har yaki ya barke

 

Leave a Reply