Malam Aminu Daurawa Yaya Kayi Tsit?

0
7

-Ibrahim Maisango
Na yiwa wannan hoto kallo na tsanaki, amma ba abinda na hango sai alamun qauna, soyayya da shauqin ganin biyu ta Zama guda.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ta gari.

Abu na biyu da ya faranta mi ni Rai kuma shine, ganin yadda shugaban Hisbah na jihar Kano ya yi tsit ba tare da nuna halin da irin sa, su ka saba bayyanawa akan ya’yan talakawa ba. Anan Ina nufin amfani da addini wajen shisshigi ga abinda bai shafe su ba, na dangane da al’amuran yau da kullum ta talakawan mabiya.

Wannan tsit da Malaman Salafiya su ka yi, ya nuna ma na cewa Allah cikin ikon sa ya fara ganar da su gaskia cewa, su guji amfani da addini wajen tsoma baki akan abunda bai shafe su ba, na rayuwar musulmi. Kullum yinwa ake yi domin halin kowa ya fito, kamar yadda wancanin ka su ka nuna a ziyarar su ta Landan.

A karshe ina taya y’an uwa na talakawan musulmi na jihar Kano da sauran jihohin arewa murnar fara shakar iskar y’anchi. Yanzu kaga batun hana gayyatar D.J yayin bikin talakawa ba bu ita kenan, an bude kofar da kowa yanzu zai bi, domin yin pre-wedding pictures, kade-kade da raye-raye yayin bukukuwa, wannan Kuma ta Kara Zama dama ga y’an uwan mu ma su harkar fina-dinai da su maida hankali wajen wakiltar al’adun mu ingantattu a fannuka daban daban na rayuwa.

n3

Leave a Reply